Ra'ayin jama'a game da aure tsakanin jinsi guda

Kwamitin hadin gwiwa a kan harkar shara`a, na majalisar dattawan Najeriya, ya saurari ra`ayoyin jama`ar kasar, game da wani kudirin doka da majalisar ke duba yiwuwar zartarwa, dokar da za ta haramta auratayya a tsakanin jinsi daya.

Kungiyoyin farar-hula da na addini da kuma daidaikun jama`a masu goyon bayan kudirin, da kuma masu sukarsa ne suka halarci zaman kwamitin, domin su bayyana matsayinsu.

Majalisar dattawan dai na kokarin zartar da kudirin ne, a daidai lokacin da Birtaniya ta yi barazanar dakatar da bada taimako ga duk wata kasar da ta ki halatta auratayya tsakanin jinsi daya.