Janar Ali Saibou ya riga mu gidan gaskiya

Allah yayi wa tsohon shugaban Nijar, Janar Ali Saibou rasuwa.

Ya rasu ne yau a birnin Yamai, bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

Shekarunsa saba'in da daya a duniya.

Ana yaba masa kan yadda ya taimaka wajen kirkiro jam'iyyun siyasa barkatai a kasar.

A ranar Laraba ake shirin yin jana'izarsa, kuma Gwamnati ta yi shelar zaman makoki na kwana ukku.