Za a ci tarar manyan kamfanonin Australia

Fiyaim Minista Julia Gillard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fiyaim Minista Julia Gillard ta Australia

Majalisar dokokin Australia ta amince da wata doka wadda ta tanadi cewa manyan kamfanonin kasar masu gurabata yanayi su dari biyar su rika biyan harajin dala ashirin da uku a kan ko wanne tan daya na iskar carbon mai guba da suka fitar.

A wata Yulin shekara ta 2012 ne dai dokar za ta fara aiki.

Masu rajin kare muhalli sun goyi bayan dokar, sai dai kuma wasu mutanen kasar da dama sun yi ta adawa da ita.

Ana dai ganin wannan doka a matsayin wata babbar nasara ga Firayim Minista Julia Gillard, wadda ta yi adawa da kudurin kafin ta hau karagar mulki.

Kasar ta Australia na samar da kashi da digi biyar cikin dari ne kawai na iska mai gubar da ake fitarwa a duniya amma kuma ita ce ta fi gurbata muhalli a tsakanin kasashe masu ci gaban tattalin arziki idan aka kwatanta da yawan al'ummarta.