Shugabannin siyasa a Girka za su gana

Firayim Ministan Girka, George Papandreou
Image caption Firayim Ministan Girka, George Papandreou

Ranar Lahadi shugabannin siyasa a Girka za su fara wani sabon yunkuri na magance matsalar siyasa da tattalin arzikin da ta dabaibaye kasar, ko da ya ke babu alamun za a cimma matsaya nan kusa.

Nan da 'yan sa'o'i ne kuma ake sa ran Shugaban kasar ta Girka, Karolos Papoulias, zai gana da jagoran babbar jam'iyyar adawa, Antonis Samaras.

Shi dai Mista Samaras ya nace cewa lallai a gudanar da zabe kafin lokacinsa, bukatar da Firayim Minista George Papandreou ya yi watsi da ita.

Mista Samaras ya goyi bayan kafa wata gwmantin gamin gambiza wadda za ta samu amincewar majalisar dokoki don karbo tallafi.

“Ina son isar da sako ga kowa a Girka da ma Turai”, in ji Mista Samaras, “cewa mun amince da yarjejeniyar zaftare basussukan da ake bin mu, mun amince da manufar yarjejeniyar, mun kuma amince da sauye-sauyen tattalin arziki”.

Sai dai ya nace cewa lallai Mista Papandreou ya yi murabus.