Za a kafa sabuwar gwamnati a Girka

Firayim Ministan Girka, George Papandreou
Image caption Firayim Ministan Girka, George Papandreou

Nan gaba a yau Litinin, Firayim Ministan Girka, George Papandreou, zai gana da babban jagoran 'yan adawa, Antonis Samaras, don yanke shawara a kan yadda sabuwar gwamnatin gamin gambiza ta kasar za ta kasance.

Jiya Lahadi ne dai Mista Papandreou ya tabbatar da cewa zai sauka daga mukaminsa a yunkurin da ake yi na magance matsalar tattalin arziki da kuma ta siyasa da ta addabi kasar.

Mutanen biyu za su tattauna ne a kan wanda zai gaji Mista Papandreou.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Girka, Elias Mosialos, ya shaidawa manema labarai cewa nan da 'yan kawanaki za a kafa sabuwar gwamnatin.

“Nan da farkon makon gobe za a kafa gwmantin ta gamin gambiza”, in ji Mista Mosialos, wanda ya kara da cewa, “Firayim Minista da jagoran 'yan adawa za su tattauna a kan wanda zai jagoranci gwamnatin da kuma ministocin da ta kunsa ranar Litinin”.

Wajibi ne dai a cimma yarjejeniya a kan kafa gwamnatin ta gamin gambiza kafin a baiwa kasar kaso na gaba na tallafin kudin da za su ceto tattalin arzikinta.

Da zarar an kafa majalisar ministoci dai za a fara kokarin amincewa da shirin tallafin na Turai ga kasar ta Girka; hakan kuma sharadi ne ga samun karin kudade.

Bangarorin biyu sun amince da 19 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da ta fi dacewa a gudanar da zabe a kasar.

Nan ba da jimawa ba ne kuma manyan jami'an Tarayyar Turai da kuma wakilai daga Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, za su je Portugal don nazari a kan irin ci gaban da kasar ta samu wajen aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar ceto tattalin arzikinta daga durkushewa, ta Euro miliyan dubu saba'in da takwas.

Jami'an dai za su yanke shawara a kan ko za a baiwa kasar kaso ba gaba na tallafin a wata mai zuwa.

Gwamnatin kasar ta Portugal, wadda ta hau karagar mulki a watan Yuni, ta bayar da sanarawar matakan tsuke bakin aljihu wadanda masu tsaurin day a ma fi abin da yarjejeniyar ta tanada.

Wakilyar BBC a babban birnin kasar, Lisbon, ta ce gwamnatin ta Portugal dai na da burin ganin ta kaucewa matsalar da kasar Giraka ta fada ciki ne.

Karin bayani