An kai hari a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sanda a Iraqi sun ce akalla mutane shidda sun rasa rayukansu a wani harin bam a Birnin Bagadaza. An kai wasu hare hare ukku a wata kasuwa mai yawan hada hadar jama'a dake Shurja a cikin birnin, yayin da jama'a ke ta hada-jhadar cefanan salla. Yanzu haka dai an kara tsaurara matakan tsaro a duk fadin Iraqi a lokacin bukukuwan babbar sallar.