An tuhumi wasu 'yan sanda da kashe Bhutto

Benazir Bhutto Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Benazir Bhutto

Wata kotu a Pakistan ta tuhumi wasu manyan jami'an 'yan sanda biyu da 'yan wasu 'yan Taliban biyar da laifin yiwa tsohuwar Frym Ministar kasar, kisan gilla a shekara ta 2007.

Mrs Bhutto ta mutu ne a wani harin bam da kuma harbin bindigogi da a kai a Rawalpindi, bayan da ta gama yin jawabi a wajen wani gangamin yakin neman zabe a Rawalpindin.

Shari'ar tasu na zuwa ne bayan shekaru hudu da afkuwar lamarin.

'Yan sandan da ake tuhumar sun hada da Saud Aziz, wanda a lokacin shi ne shugaban 'yan sanda a garin Rawalpindi.

Ana zargin Mr. Aziz da kin kare tsohuwar pira ministar, wadda a lokacin ke hamayya da shugaban kasar mai ci, wato Pervez Musharraf.

Duka mutane bakwan da ake tuhuma sun musanta zargin da ake musu.