Amurka ta ce Boko Haram na shirin kai hari

Hakkin mallakar hoto AFP

Ofishin jakadan cin Amurka a Najeriya ya ce ya samu bayanan da ke cewa kungiyar Jama'atu ahlil sunnah liddawati wal jihad, na shirin kaddamar da hare hare akan manya manyan otel otel da wasu wurare a babban birnin kasar Abuja a wannan makon.

Ofishin jakadan cin Amurkar ya wallafa wannan sanarwar ce a shafin sa na yanar gizo inda ya gargadi duk 'yan Amurka dake kasar musanmanma wadanda ke Abuja da suyi taka tsan tsan.

Wannan gargadin dai na zuwa ne kwanani kadan bayan wasu hare hare da tashin bama bamai da suka hallaka fiye da mutane 60 a garin Damaturu dake arewan Nijeriya.

Karin bayani