Amnesty International ta yi Allah-wadai da Uganda

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin Uganda ke amfani da matakan danniya don murkushe adawa.

Kungiyar ta ce ana musgunawa da kuma kame 'yan jarida da 'yan adawa masu fafutuka babu gaira babu dalili idan duka kuskura suka soki hukumomin kasar.

Kungiyar ta Amnesty ta ce yanzu dai an haramta yin gangami a kasar ta Uganda.

Minisatr yada labarai ta kasar, Mary Karooro, ta ce za ta mai martani bayan ta yi nazari a kan rahoton da kungiyar ta Amnesty ta fitar.