Girka za ta kada kuri'ar akan tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu adawa da shirin tsuke bakin aljihu a Girka

Yarjejeniyar da aka cimma don magance matsalar bashin da ta dabaibaye wasu kasashe masu amfani da kudin euro ta fada cikin rudani sakamakon wata sanarwar ba zata cewa kasar Girka za ta gudanar kuri'ar raba-gardama a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihu.

Kuri'ar jin ra'ayin a kasar ta Girka dai ta nuna cewa akasarin jama'a ba sa goyon bayan matakan tsuke bakin aljihun.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan yunkuri na Fira Ministan Girka George Papandreou ka iya yin kafar ungulu ga tsare-tsraen da shugabannin Tarayyar Turai suka yi a Brussels a makon da ya gabata.

Mista Papandreou dai ya ce al'ummar Girka ce za ta yanke shawara ta karshe a kan al'amarin.

"Wajibi ne a kanmu mu ba da muhimmanci ga rawar da talakawa za su taka mu kuma nuna cewa da bazarsu mu ke rawa." In ji Papandreou.

Wannan dai za'a iya cewa shine abu na karshe da shugabanin kasashen Turai ba su tsaba tsammanin zai faru ba. Pira Ministan Girka, bayan ya fuskanci matsin lamba a gida ya ce mutanen sa za su kada kuri'ar raba gardama domin jin ra'ayinsu wajen amincewa da gudunmuwar da za'a ba kasar a karo na biyu.

Annan gani dai wannan mataki zai kwantar da hankali jama'a a kasuwannin hanayen jari, kafin shugabanin kasashen G20 su gana a wani taro da za su yi a Faransa a wannan makon.

A yanzu haka dai ana ganin ya kamata ne dai ana aiwatar da manufofin kasashen ba wai tattaunawa akan yiwuwar aiwatar da shirin da aka cimma ba.

Tun a lokacin da aka cimma yarjejeniya tsakanin shugabanin kasashen Turan, ruwan da ke kan bashin da Italiya na karuwa ne a maimakon ya yi kasa.

Masu sanya hannayen jari dai na ganin ko kudin da aka alkawarin baiwa Girka a matsayin gudunmuwa ba zai isa ba.

Har yanzu dai ba'a bayyana yadda tsarin kuri'ar raba gardamar za ta kasance ba, amma ana ganin yawan al'ummar Girka na iya wargazar da shiri gabaki daya.