An daure sojin Amurka a Koriya ta kudu

Hakkin mallakar hoto US Army
Image caption Akwai kusan sojojin Amurka dubu ashirin a kasar Koriya ta kudu

Rahotanni daga kasar Koriya ta kudu sun ce an daure wani sojan Amurka a gidan kaso na tsawon shekaru goma bayan an same shi da laifin yiwa wata mata fyade.

Sojan ya yiwa matar fyade a kusa da sansanin sojojin Amurka da ke kasar.

Wata kotu a kasar Koriya ce ta yanke hunkunci, bayan a zargi jami'in tsaron da aikata laifin a watan Satumba.

Amurka dai nada dakarun tsaro kusan dubu ashirin da takwas a koriya ta kudu.

Rahotanni dai sun ce sojan ya shiga gidan wata yar kasar koriya ne mai shekarun haihuwa 18, inda ya yi mata fyade na tsawon lokaci.

Alkalin kotun ya bayyana abun da sojan ya aikata a matsayin babban laifi na fitan hankali wanda kuma ya keta hakkin bil'adama.

Wannan dai shine hukunci mafi tsauri da aka taba dauka akan soji Amurka a kasar Koriya ta kudu.

A baya dai ana gudanar da zanga zanga ne mai karfi idan an zargin sojojin Amurka da aikata manyan laifuka, musamman ma idan ana jayayya ko wacce kasa za ta yi musu hukunci.

Amurka dai na da iko akan sojojin ta dake Koriya, saboda wata yarjejeniya da kasashen biyu su ka cimma.

Jami'an sojin na Amurka sun ce suna mutunta duk wata bukata da gwamnatin Koriya ta kudu ta nema na hukunta duk wani sojin Amurka da aka samu da aikata wani babban laifi.