Muhawara kan haramta auren jinsi daya a Najeriya

Gay
Image caption Masu adawa da auren jinsi guda a kasashen Turai

A Najeriya, bangarorin al`uma daban-daban na bayyana ra`ayinsu game da wani kudirin doka da majalisar dattawan kasar ke duba yiwuwar zartarwa, wanda zai haramta auratayya a tsakanin jinsi daya.

A jiya ne dai kwamitin majalisar ya yi wani zama na sauraron ra`ayin jama`a, inda kungiyoyin farar-hula da na addini da kuma daidaikun jama`a masu goyon bayan kudirin da kuma masu sukarsa suka halarci zaman.

Majalisar dattawan dai na kokarin zartar da kudirin ne a daidai lokacin da kasar Birtaniya ta yi barazanar cewa za ta dakatar da ba da taimako ga duk wata kasar da ta ki amincewa da dokar halalta auratayya tsakanin namiji da namiji.

Duk da irin bambance-bambancen da akan samu a tsakanin mabiya manyan addinin Najeriya biyu, wato da addinin musulunci da na Kirista ta fuskar manufofin kasa, a wannan karon za a iya cewa bakin addinan ya zo daya, saboda dukansu babu wanda ya sassauta wajen yin tir da duk wani yunkuri na halalta auratayya a tsakanin jinsi daya.

Shugabanin addinia

Hajiya Salamatu Ahmad na daga cikin wadanda suka wakilci kungiyar mata Musulmi, wato FOMWAN a wajen sauraron ra`ayoyin jama`ar.

"Gaskiya addini ta haramta auren jinsi daya, kuma mun gaya musu bamu amince da wannan doka ba." In ji Salamatu Ahmad

Shi ma reshen mabiya addinin kirista `yan darikar Katolika, wanda sakatare-janar na kasa ya wakilta cewa ya yi.

"Bisa koyarwar Littafi mai tsarki ana aure ne tsakanin namiji da mace, kuma ita ce akidar da darikar katolika ta runguma, haka kuma za ta ci gaba da tafiya a kan wannan tafarkin.

"Idan aka halalta auratayya tsakanin jinsin daya, to za'a bude kofar da wata rana Uba ma sai ya ce zai auri `yar cikinsa, ko kuma uwa ta auri dan da ta haifa." In ji Sakatare Janar darikar Katolika na kasa.

Kungiyoyin fararen hula

Wasu Kungiyoyin farar-hula masu kare hakkokin bil`adama da takwararsu ta lauyoyin Najeriya da sauran dangoginsu sun bayyana nasu ra`ayin, inda suka nisanta kansu daga halalta auratayya tsakanin jinsi daya, suna jaddada cewa yin hakan ya saba wa al`udun Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki daya.

Sai dai wata makala da wata mai suna Dr Otibo Obinwa ta gabatar a madadin masu goyon bayan a halalta auratayya tsakanin jinsi dayan ta ja hankalin jama`a, musamman yadda ta kai ga barkewa da kuka, sakamakon abin da ta bayyana cewar al`uma na jahiltarsu.

"Sanya auratayya tsakanin jinsi daya a sahun miyagun laifuka ya maida mu `yan-gudun-hijira a kasarmu ta haihuwa. Wannan azabtarwa ce." In ji Dr Otibo Obinwa.

Shugaban kwamitin Senata Umaru Dahiru ya ce kwamitin za ta rubuta rahoton abubuwan da ya tattaro a zaman jin bahasin jama'a a gaban Majalisar.

Duk da irin matsin-lambar da wasu kasashen yammacin duniya ke yi game da zartar da dokar da za ta halalta auratayya tsakanin jinsi daya, masu lura da al`amura na ganin cewa akwai bukatar `yan majalisar Najeriyar su yi kaffa-kaffa da wannan zazzafar muhawarar, saboda al`umar kasar kan dauki duk wani abin da ya shafi addini da zafin gaske.