Damuwa kan kuri'ar kasar Girka

Girka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu adawa da shirin tsuke bakin aljihu a Girka

Darajar hannayen jari ta fadi warwas bayan da kasar Girka ta ce za ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan shirin tattalin arzikin da hukumomin Turai suka gabatar mata.

Kuri'ar jin ra'ayi a kasar ta Girka dai ta nuna cewa aka sarin jama'ar kasar ba sa goyon bayan matakan tsuke bakin aljihun da gwamnati ke dauka.

Sai dai kuma kashi 70 cikin dari na a'ummar kasar suna son Girka ta ci gaba da amfani da kudin bai daya na euro.

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa zai tattauna ta waya da shugabar Jamus Angela Markel, kan lamarin.

Tsohon ministan kudi na Jamus Rainer Bruderle, ya ce ya kadu da matakin na Girka.

Yarjejeniyar da aka cimma don magance matsalar bashin da ta dabaibaye wasu kasashe masu amfani da kudin euro ta fada cikin rudani sakamakon wata sanarwar ba zata cewa kasar Girka za ta gudanar kuri'ar raba-gardama a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihu.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan yunkuri na Fira Ministan Girka George Papandreou ka iya yin kafar ungulu ga tsare-tsaren da shugabannin Tarayyar Turai suka yi a Brussels a makon da ya gabata.

'Rawar da talakawa za su taka'

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Fira MInistan Girka George Papandreou na fuskantar matsin lamba

Ana gani dai wannan mataki zai kwantar da hankali jama'a a kasuwannin hanayen jari, kafin shugabanin kasashen G20 su gana a wani taro da za su yi a Faransa a wannan makon.

Amma yanzu cikinsu ya fara durar ruwa, ganin cewa rashin tabbas din da ake fama da shi a baya ya dawo.

Mista Papandreou dai ya ce al'ummar Girka ce za ta yanke shawara ta karshe a kan al'amarin.

"Wajibi ne a kanmu mu ba da muhimmanci ga rawar da talakawa za su taka mu kuma nuna cewa da bazarsu mu ke rawa." In ji Papandreou.

Wannan dai za'a iya cewa shi ne abu na karshe da shugabanin kasashen Turai ba su taba tsammanin zai faru ba.

Fira Ministan Girka, bayan ya fuskanci matsin lamba a gida ya ce mutanen sa za su kada kuri'ar raba gardama domin jin ra'ayinsu wajen amincewa da gudunmuwar da za'a ba kasar a karo na biyu.

A yanzu haka dai ana ganin ya kamata ana aiwatar da manufofin kasashen ne ba wai tattaunawa a kan yiwuwar aiwatar da shirin da aka cimma ba.

Tun a lokacin da aka cimma yarjejeniya tsakanin shugabanin kasashen Turan, ruwan da ke kan bashin da Italiya na karuwa ne a maimakon ya yi kasa.

Masu sanya hannayen jari dai na ganin ko kudin da aka alkawarin baiwa Girka a matsayin gudunmuwa ba zai isa ba.

Har yanzu dai ba'a bayyana yadda tsarin kuri'ar raba gardamar za ta kasance ba, amma ana ganin yawan al'ummar Girka na iya wargazar da shirin gabaki daya.

Karin bayani