Kotu ta yi watsi da karar CPC kan zaben Jonathan

CPC
Image caption Jam'iyyar CPC ce ta zo ta biyu a zaben na watan Afrilu

Kotun daukaka kara a Najeriya ta yi watsi da karar da jam'iyyar CPC ta shigar tana kalubalantar zaben shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP.

Duka alkalan kotun guda biyar sun amince wajen tabbatar da zaben da aka yi wa Jonathan a ranar 16 ga watan Afrilu, sannan ta yi watsi da kiran da jam'iyyar adawa ta CPC ta yi na a soke zaben a wasu sassan kasar.

An bayyana Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben 16 ga watan Afrilu da kashi 59 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Sai dai mutumin da ke binsa a zaben, janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, wanda ya samu kashi 32 cikin dari ya ki amince wa da sakamakon zaben.

A don haka ne jam'iyyar ta sa ta Congress for Progressive Change (CPC) , ta shigar da kara domin kalubalantar zaben a watan Mayu.

Karin bayani