Binciken ra'ayoyin jama'a da BBC ta gudanar

Image caption Tambarin BBC

Wani binciken jin ra'ayoyin jama'a da BBC ta gudanar a kasashe 25 ya gano cewa ana samun bambancin ra'ayi game da yadda tsarin tattalin arziki ya ke.

Binciken ya nuna cewa jama'a a akasarin kasashen da ke da karfin tattalin arziki na nuna rashin kwarin gwiwarsu game da ci gaban tattalin arzikinsu, yayin da a kasashe masu tasowa kuwa, jama'a ke nuna kwarin gwiwa.

A kasashen Japan, da Faransa da kuma Burtaniya, yawan mutanen da ke sa-ran ci gaban tattalin arziki basu wuce kashi daya cikin dari ba, yayin da a kasashe masu tasowa, masu nuna kwarin gwiwa suka zarta wadanda basu da kwarin gwiwa.

Misali, a Najeriya fiye da kashi saba'in na mutanen da aka yi bincike a kansu sun nuna kwarin gwiwarsu game da tsarin tattalin arziki, sabanin kasar Pakistan inda wadanda basu da kwarin gwiwa ke da dan karamin rinjiye.