Hari kan ofishin jaridar Charlie Hebdo a Faransa

Charlie Hebdo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Editan jaridar ya ce bayanan da suka buga ne suka sa aka kai musu harin

'Yan sanda a kasar Faransa sun ce an lalata ofisoshin jaridar Charlie Hebdo da ake bugawa a kasar, bayan da ta yi batanci ga Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam.

Harin ya zo ne kwana guda bayan da mujallar ta wallafa batancin a shafinta na farko.

Mujallar ta ce ta yi hakan ne domin nuna "murna" ga nasarar da jam'iyyar Musulunci ta An-Nahda ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Tunisia a watan da ya gabata.

An ambato editan jaridar yana cewa: "A yanzu bamu da jarida. An lalata dukkan kayan aikinmu."

Wani da ya shaida lamarin Patrick Pelloux, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an jefa wani bam din kwalba ta taga a ginin, abinda kuma ya sa wuta ta tashi a wurin da kwamfiyutocin ofis din suke.

"An lalata komai a wurin," a cewarsa.

Ba a samu labarin wani ya samu rauni ba a harin.

Harzuka jama'a

Masu satar bayanan kwamfiyuta sun kuma lalata shafin intanet na jaridar, inda aka wallafa bayanai da harshen Turanci da Turkanci da ke yin Allah wadai da mujallar.

Jaridar ta wannan makon an yi mata take ne da ke yin izgili kan tsarin shari'ar Musulunci.

A ka'idar addinin Musulunci, yin batanci ga Annabi Muhammad babban sabo ne da ke dauke da hukuncin kisa.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, jaridar ta ce ta yi hakan ne saboda nasarar da jam'iyyar Musulunci ta samu a Tunisia, da kuma bayanin cewa za a yi amfani da shari'ar Musulunci a sabuwar gwamnatin kasar Libya.

Mujallar ta musanta cewa ta yi hakan ne domin harzuka al'ummar Musulmi.

Sai dai wakilin BBC a Faransa Hugh Schofield, ya ce mujallar ta Charlie Hebdo ta yi kaurin suna wajen aikata al'amuran da kan harzuka jama'a.

A shekara ta 2007 ma jaridar ta maimaita wallafa zanen batancin da aka yi wa Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam, wanda wata jaridar kasar Denmark ta wallafa - wanda kuma ya haifar da rikici a sassan duniya daban-daban.