Ministan kudi na Jamus ya gargadi Girka

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption George Papandreou

Faransa ta ce, ya kamata kasar Girka ta yanke shawara ba tare da bata lokaci ba, a kan ko tana son ta ci gaba da kasancewa a cikin yankin kudin bai daya na Euro.

Gargadin ya biyo bayan irinsa da kasar Jamus ta yi, kuma ya zo ne 'yan awoyi kamin tattaunawar gaggawar da ake shirin yi, a kan shirye shiryen kasar ta Girka, na yin kuri'ar raba-gardama, a kan matakan yin belin nata. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce, shawarar da Girka ta yanke, ta zo masu hakanan kwatsam. A yanzu dole ne su sami karin haske, don su san matakin da za su dauka.

An cimma yarjajeniya a kan yadda za a yi belin kasar ta Girka ne, bayan an dauki dogon lokaci ana ta sasantawa.

Kuma kasashen duniya da dama na ganin cewa, shirin belin na da mahimmancin gaske ga farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya.

Yanzu haka dai majalisar dokokin kasar ta Girka ta fara muhawarar kwana ukku, wadda za ta kai ga jefa kuri'ar amincewa ko kin amincewa da gwamnatin Pirayim minista George Papandreou.

An shirya muhawarar ce, bayan da Pirayim ministan yayi sanarwar ba-zata, a kan shirya kuri'ar raba-gardama, dangane da yarjajeniyar da Tarayyar Turai ta cimmawa a makon da ya wuce, game da yin belin kasar Girkan.

Jam'iyyar Mr Papandreou ta 'yan gurguzu, tana da rinjayen kujeru biyu ne kawai a majalisar dokokin.

Kuma a cewar masu nazari, mai yiwuwa gwamnatin ba za ta kai labari ba.

Da yawa daga cikin mambobin jam'iyyar ta George Papandreou suna adawa da shirya kuri'ar raba-gardamar, tare da yin kira a gare sa da yayi murabus.

Majalisar zartarwar kasar Girka ta amince da shawarar da Firaministan kasar, George Papandreou, ya gabatar mata inda ya bukaci a gudanar da kuri'ar raba-gardama game da bashin da Tarayyar Turai ke son baiwa kasar.

Tarayyar Turan ta ce za ta baiwa Girka bashin ne da nufin ceto tattalin arzikinta daga durkushewa, amma dole ne kasar ta amince da wasu matakan tsuke-bakin aljihunta.

Matakan dai sun hada da kara kudin ruwa da rage ma'aikata, matakan da tuni 'yan kasar suka yi watsi da su.

Mr Papandreou ya shaidawa taron da ya gudanar da ministocinsa cewa za a gudanar da kuri'ar raba-gardamar ce don ganin ba a tilastaswa 'yan kasar amincewa da duk wani matakin tsuke-bakin aljihun gwamnati ba.

Ya ce za su yi amfani da sakamakon kuri'ar raba-gardamar wajen aiwatar da tsare-tsaren ci gaban tattalin arziki na kasar.