Williams na son sauyi a tsarin tattalin arzikin duniya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rowan Williams

Shugaban cocin Anglican, Rowan Williams, ya yi kira ga kasashe su aiwatar da sauye-sauye a tsarin tattalin arzikinsu.

Rowan William na yin tsokaci a karon farko, tun bayan da wasu mutane suka gudanar da zanga-zanga don bayyana rashin jin dadinsu ga abin da suka ce rashin adalci ne da kuma cuwa-cuwa a tsarin tattalin arzikin duniya.

Sun kafa sansani a majami'ar Saint Catedral a tsakiyar watan Oktoba.

Tsoma-bakin da Mr William ya yi, ya nuna cewa yana goyon bayan wadanda ke korafe-korafe game da tsarin tattalin arzikin duniya.

Ya goyi bayan wata sanarwa da fadar Vatican ta fitar a makon jiya, wacce ta goyi bayan sanya haraji a tsarin tattalin arziki, da kuma raba hada-hadar banki ta yau-da-kullum da sauran harkokin kasuwanci wadanda ke da matukar hadari, kana da kara yawan jarin bankuna da kudaden jama'a.

Ya ce wadannan matakai ba za su kawar da tsarin raji-hujja ba, sai dai ya kara da cewa, za su yi kyakkyawan tasiri ga tsarin tattalin arzikin duniya.