Syria ta amince da shawarwarin kungiyar Larabawa

Taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taron kungiyar kasashen Larabawa

Kungiyar kasashen Larabawa ta ce, kasar Syria ta amince da shawarwarin da ta gabatar, na kawo karshen tashe tashen hankulan siyasar da aka kwashe watanni bakwai ana yi a Syriar.

Da yake karanta sanarwar, bayan taron ministocin kungiyar a birnin Alkahira, Pirayim ministan Qatar, Sheikh Hamad bin Jassim al-Thani, ya ce, gwamnatin Syria za ta janye tankunan yaki daga kan tituna.

Haka nan kuma ta ya ce gwamnatin Syriar za ta saki fursunonin siyasa, sannan za ta kyale manema labarai na kasashen waje su je kasar, domin sa ido akan abubuwan da ke faruwa.

Pirayim ministan Qatar din ya kuma shaidawa 'yan jarida cewa, kungiyar kasashen Larabawan za ta shiga tsakanin gwamnatin Syrian da kuma 'yan adawar kasar.

Ya ce kuma za a shirya abinda ya kira, tattaunawa a tsakanin 'yan kasar ta Syria, nan da makonni biyu masu zuwa.