An rantsar da shugaba Paul Biya a Kamaru

A Jumhuriyar Kamaru yau ne aka rantsar da zababben shugaban kasar, Paul Biya.

Bikin rantsarwar, wanda aka yi a zauren majalisar dokokin kasar, ya ba Mr Biya din, damar yin wani sabon wa'adin mulki na shekaru bakwai.

Sai dai babu wani shugaban kasa na waje da ya halarci bikin; haka shi ma jagoran 'yan adawan kasar, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben da aka yi a watan jiya, John Fru Ndi, ya kauracewa bikin.

Shugaba Biya dai ya lashe zaben da aka yi a watan jiya ne da gagarumin rinjaye, inda ya samu kusan kashi saba'in da takwas cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben.