Takaddama tsakanin Najeriya da Birtaniya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage adadin jiragen kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Biritish Airways, da ke sauka da tashi a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas daga ranar 8 ga wannan watan.

Ma'aikatar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon hada-hadar da ake yi a filin saukar jiragen na Legas daga watan Nuwamba - zuwa karsheh shekara.

Sai dai da ma a 'yan kwanakin nan an samu rashin jituwa tsakanin hukumomin Burtaniya da wasu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya.