Harin kunar bakin wake a Maiduguri

Harin kunar bakin wake a Maiduguri
Image caption Birnin Maiduguri ya sha fama da hare-hare daban-daban

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan hedkwatar rundunar kiyaye zaman lafiy ta JTF a garin Maiduguri na Najeriya, kamar yadda wata majiyar soji ta tabbatar wa BBC.

Maharin ya mutu kuma wani soja guda daya ya samu rauni a harin na babban ofishin JTF.

An kai wasu hare-haren bama-baman uku a wasu sassa daban-daban na jihar ciki harda wajen wata kwaleji.

Da kuma ofishin hukumar leken asiri ta SSS, da hanyar Baga wadda ba ta da nisa sosai da wani babban barikin soji.

Kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan wadannan a birnin Maiduguri da kuma wasu sauran sassan kasar.

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar hadin gwuiwar ta JTF tace tana samun nasara a yekuwar da ta yi na mazauna birnin na Maiduguri su mika mata makamansu.

Wani mazaunin garin na Maiduguri Malam Bashir Muhammad Shuwa, ya shaida wa BBC cewa ya ga hayaki yana tashi a wasu unguwanni da abin ya faru, kuma sojoji na binciken ababen hawa a wurare da dama.

Babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki nauyin kai wannan hari kawo yanzu.

Amma mai magana da yawun rundunar kiyaye zaman lafiya Laftanal Kanal Hassan Ifijeh Mohammed, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, sun dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram.