Gwamnatin Girka ta sauya matsayinta

Ma'aikatar kudin kasar Girka ta ce an dakatar da shirin nan na shirya kuri'ar raba gardama dake ta janyo kace-nace kan shirin bada tallafi da matakan tsuke bakin aljihu.

Shawarar wadda praministan kasar George Papandreou ya bada sanarwarta a farkon wannan mako ta janyo maida martani cikin fushi daga shugabannin kasashen Turai, wadanda ke fargabar cewa, matakin zai kawo cikas ga shirin tallafin da aka amince da shi.

Sanarwar kuma ta haddasa rudani a kasuwar hannayen jari, wadda ta yi kasa, amma a yanzu ana cewa ta fara murmurewa sakamako n sanarwar.