An sace jirgi dauke da man fetur a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga yankin Naija Delta da ke Kudu maso kudancin Najeriya, na cewa wasu masu fashi a teku sun sace wani jirgin ruwan dakon man fetur a yankin.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da matatar mai da ke birnin Fatakwal, inda ake kyautata zaton cewa ana ci gaba da tsare direbobin jirgin mai suna "the Halifax".

Direbobin dai baki ne 'yan kasashen waje.

Masu sharhi sun bayyana cewa matsalar sace-sacen jiragen ruwa da ke dakon mai da kuma garkuwa da matuka jiragen na dada kamari a yankin, inda masu fashi a teku kan farma jiragen ruwan da ke fitowa daga Najeriya.

A mafi yawan lokuta akan sace man da ke cikin jirgin ne kafin daga bisani a saki jirgin da sauran fasinjojin da ke cikinsa.