Sojojin Sudan sun fatattaki 'yan tawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Sudan

A kasar Sudan, sojojin gwamnati sun karbe wani muhimmin gari maisuna Kurmuk daga hannun 'yan tawaye a jihar Blue Nile.

Jihar dai na da iyaka ne da sabuwar kasar Sudan ta Kudu, kuma garin na Kurmuk, nan ne magoya bayan Sudan People's Liberation Movement ke da karfi.

Tun a watan Satumba ne dai fada ya barke yayin da sojojin gwamnatin Sudan suka nemi nuna iko a yankin bayan da kasar Sudan ta kudu ta samu 'yancin kai a watan Yuli.