Yau ce ranar Arafat

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakin Ka'aba

A yau Asabar ce ake hawan Arafat a birnin Makka na kasar Saudi Arabia, wanda shi ne ginshikin aikin hajj.

Tun a jiya Juma'a ne dai maniyyatan da suka fito daga sassa daban-daban na duniya suka isa Muna a wani bangare na fara aikin Hajji gada-gadan.

Rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a fadin kasar, inda maniyyata fiye da miliyan biyu da rabi ke fara aikin Hajji.

Aikin hajji dai na daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar da ake bukatar dukkan musulmi mai iko ya gudanar, akalla sau daya a rayuwarsa.