Bam ya kashe mutane da dama a Nigeria

Yobe
Image caption Hare-haren sun dimauta mazauna birnin na Damaturu

Rahotanni sun ce akalla mutane 60 ne aka kashe a wasu hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Damaturu na jihar Yobe dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a hedkwatar 'yan sanda ta birnin da kuma wasu rukunin gidaje da rundunar tsaro ta musamman ke amfani da su. Wakilin BBC Naziru Mika'ilu a Abuja, ya ce an shafe daren jiya ana jin karar harbe-harbe a birnin, kuma ana cikin zaman dar-dar.

Wannan harin dai ya zo bayan wani makamancinsa da aka kai kan jami'an tsaro a birnin Maiduguri - mai nisan kilomita 130 daga Damaturu.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ya ga gawarwaki da dama a babban asibiti na birnin.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Yobe ya ce harin ya baiwa mazauna garin mamaki.

Wasu rahotannin kuma na cewa kusan mutane 60 ne suka rasa rayukansu.

Karin bayani