Firayim Ministan Girka ya tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto papandreou
Image caption George Papandreou

Firayim Ministan Girka, George Papandreou, ya samu nasara game da kuri'ar yankan kaunar da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada a kan gwamnatinsa.

Wasu 'yan majalisa da kuma 'yan jam'iyun adawa sun so ne ya sauka daga kan mukaminsa sannan ya gudanar da zabe cikin gaggawa bayan da suka zargi gwamnatinsa da gaza kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.

Mr Papandreou ya gargadi 'yan majalisar cewa gudanar da zabe cikin gaggawa ka iya zama wani babban bala'i ga kasar da ke fama da matsalar basussuka.

'Yan majalisa 153 ne suka goyi bayansa, kana guda 145 kuma suka ki goyo bayansa, cikinsu kuwa har da da dama daga cikin 'yan jam'iyarsa .

Shi dai Mr Papandreaou ya so ne a gudanar da kuri'ar raba-gardama game da batun bashin da kungiyar Tarayar Turai ke shirin baiwa kasarsa, sai dai ya janye shirin nasa bayan da ya fuskanci matsin-lamba daga cikin kasar da ma kasashen Turai da ke amfani da kudin bai-daya na euro.