Syria ta saki fursunoni fiye da 500

Shugaba Bashar Al Asad na Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Syria ta sako wasu fursunonin siyasa gabanin babbar sallah

A yau asabar Kasar Syria ta bada sanarwar cewar ta saki mutane dari biyar da hamsin da uku wadanda aka tsare lokacin tashin hankali a kasar.

Syrian tace ta dauki wannan mataki ne saboda girmama bikin babbar sallah. Sanarwar tace ba a sami wadanda aka saki da laifi ba

A waje daya kuma Sakatare Janar na kungiyar kasashen larabawa Nabil -Al -Arabi yace duk wata gazawa da larabawa suka yi wajen warware rikicin kasar Syria ka iya zama wani babban bala'i ga yankin.

Tunda farko dai gwamnatin kasar Syrian ta amince ta janye sojojinta dake kan titunan kasar, ta kuma soma tattaunawa tare da 'yan adawa, amma sai dai har ya zuwa yanzu, ba a sami lafawar tashin hankali ba.

Kungiyar dake sa- ido akan hakkin dan Adam ta kasar Syrian, tace an kashe mutane uku yau asabar a birnin Homs. An kuma hallaka wasu sojojin dake goyan bayan gwamnati su hudu a lokacin wani artabu a arewacin kasar