Bam ya kashe fiye da mutane 60 a Yobe

Yobe
Image caption Hare-haren sun dimauta mazauna birnin na Damaturu

Fiye da mutane 65 ne aka kashe a wasu hare-haren bama-bamai da kungiyar nan ta Boko Haram ta kai a birnin Damaturu na jihar Yobe dake Arewacin Najeriya.

Mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross, ya shaida wa BBC cewa mutane 53 sun mutu a Damaturu babban birnin jihar Yobe, sannan wasu goma suka rasa rayukansu a wani garin na daban.

Lamarin ya auku ne bayan da wasu mahara suka tayar da wasu abubuwa da ake kyautata zaton bama-bamai ne aa wasu gine-ginen gwamnati cikin har da babban ofishin 'yan sanda na birnin.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a hedkwatar 'yan sanda ta birnin da kuma wasu rukunin gidaje da rundunar tsaro ta musamman ke amfani da su. Wakilin BBC Naziru Mika'ilu a Abuja, ya ce an shafe daren jiya ana jin karar harbe-harbe a birnin, kuma ana cikin zaman dar-dar.

Daya daga cikin jami'an agaji na kungiyar musulunci ta Jam'atun Nasrul Islam, ya shaida wa wakilinmu cewa sun tattara gawarwaki 96 da harin ya ritsa da su a babban asibitin birnin na Damaturu.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ya ga gawarwaki da dama a babban asibiti na birnin.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Yobe ya ce harin ya baiwa mazauna garin mamaki.

Ko a ranar Juma'a an kai harin kunar bakin wake a birnin Maiduguri - matattarar kungiyar Boko Haram, inda uku daga cikin maharan suka mutu.

Karin bayani