Joe Frazier na fama da cutar sankaran hanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joe Frazier

Tsohon zakaran demben boxing na Amurka Joe Frazier na fama da cutar sankaran hanta.

Manajan tsohon dan demben ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an gano cutar ne a jikin Frazier wasu makwanni da su ka wuce.

"A gaskiya zan yi karya idan nace ciwon bai yi tsanani ba." In ji Manajan dan demben, Leslie Wolf.

Tsohon dan demben mai shekarun haihuwa 67 ya rike kambun dan demben duniya ne tsakanin shekarar 1970 da kuma 1973.

Shine kuma dan dembe na farko da ya doke Muhammad Ali a shekara ta 1971.

Daga baya dai Muhammed Ali ya doke sa a haduwa biyu da su ka yi.

Mista Wolf ya ce Frazier na jinya ne a wani asibiti da ke Philadelphia.