Iran ta ce Amurka na neman goyon bayan kai mata hari

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad ya zargi Isra'ila da Amurka da kokarin neman goyon baya, domin kai ma Iran din farmaki.

Wannan furuci da ya yi ma wata jaridar kasar Masar, ya biyo bayan wasu kalamai ne na shugaban Isra'ilar, Shimon Peres, inda yake cewa, yuwuwar daukar matakin soja a kan Iran na kara kusantowa, saboda tana dab da kera makaman nukiliya.

Ita dai Iran ta ce shirin nukiliyarta ba na kera makamai ba ne.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce duk wani hari a kan Iran zai kasance babban kuskure, wanda kuma ba a san irin sakamon dazai biyo baya ba.