Watakila Berlusconi ya yi murabus a gaba

Praminista Berlusconi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Praminista Berlusconi

An bayar da rahoton cewar Shugaban kasar Italiya ya ce Praminista Silvio Berlusconi yayi alkawarin yin murabus, to amma fa sai bayan majalisar dokoki ta zartas da sauye sauyen tattalin arzikin da kungiyar Tarayyar Turai ta bukata.

Tun farko dai Mr Berlusconi ya rasa rinjayen da yake da shi a Majalisar dokokin, a wata muhimmiyar kuri'a kan kasafin kudi.

An dai yi kuri'ar ne a wani lokaci da matsalar kudin kasar ta Italiya ta kara tabarbarewa.

Shugaban adawa, Pier Luigi Bersani, ya yi gargadin cewar Italiya za ta iya rasa dama a kasuwannin kudi a cikin 'yan kwanaki.