Za a mika praminista Baghdadi ga Libya

Wata kotu a Tunisia ta yanke hukuncin cewa a tasa keyar Al -Baghdadi Ali Al-Mahmoudi, Pirayim Ministan Libya a karkashin Kanar Gaddafi, zuwa Libya.

Sabbin mahukunta a can na son gurfanar da Al- Mahmoudi a gaban shari'a.

Lauyansa ya bayyana hukuncin a matsayin mai nasaba da siyasa.

Ya ce Al -Mahmoudi, wadda ke da shekaru saba'in a duniya, zai kasance cikin hadari saboda abinda ya kira yamutsi a Libya.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bukaci Tunisia da kada ta mika Al -mahmoudi.