Hankalin jama'a na tashe a garin Kafanchan

'Yansandan Najeriya
Image caption Tsugune ba ta kare ba a jihar Kaduna

A Kafancan da ke jahar Kaduna har yanzu ana can ana zaman fargaba sanadiyyar wani rikici tsakanin matasa Musulmi da matasa mabiya addinin Kirista.

Tuni gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita, bayan da aka yi dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu tare da kone-kone.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan irin asarar da aka yi ta dukiya ko kuma ta rayuka a wannan rikici.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne bayan da aka samu rahoton halaka wani dan Achaba musulmi.

Sarkin garin ya ce ana zullumin abin da zai auku cikin dare saboda karancin jami'an tsaro.

Sai dai Mr Reuben Buhari, kakakin gwamnan jihar ta Kaduna, ya ce an kafa dokar hana fitar ta ba-dare-ba-rana, yana mai cewa a yanzu an yayyafa wa kurar rikicin ruwa