Amurka ta janye gargadin da taiwa mutananta

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya janye gargadin da ya yi wa 'yan kasar ranar Lahadin da ta gabata na su kaurace wa ziyartar wasu manyan Otel guda uku dake Abuja babban birnin kasar, saboda ya samu bayanan da ke nuna cewa ana shirin kai musu hari.

Ofishin jakadancin ya ce ya janye gargadin ne saboda an samu ingantuwar tsaro a kewayen Otel-Otel din da kuma muhimman hanyoyin birnin.

A makon da ya gabata ne aka kai wasu jerin hare hare a wasu jahohin arewacin Najeriya, inda sama da mutane 65 suka rasa rayukansu.

Matsalar tsaro a Najeriya dai na ci gaba da ciwa hukumomin kasar tuwo a kwarya, dukkuwa da irin matakan shawo kan matsalar da suke cewa suna yi.