Girka ta zabi sabon pira minista

Lucas Papandemos Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lucas Papandemos

A kasar Girka an bayyana sunan Lukas Papademos, a matsayin praministan rikon kwarya. A da Mr Papademos, mataimakin shugaban babban bankin tarayyar turai ne.

Yanzu haka shugaban kasar ya neme shi da ya kafa sabuwar gwamnation hadin kan kasa, gwamnatin da zata aiwatar da yarjejeniyar da aka cinma da tarayyar turai kan agajin da za a baiwa Girkar.

Hakan na faruwa ne yayinda Tarayyar Turai ta rage girman habakar tattalin arzikin da aka yi hasashe a kasashe masu amfani da kudin euro a badi, daga kashi daya da digo takwas cikin dari zuwa rabin kashi guda kacal cikin dari.

Wani babban jami'i na tarayyar turai ya yi gargadin cewa an samu tsaiko a bunkasar tattalin arzikin, kuma ana fuskantar hadarin sake fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

Karin bayani