Allen Sirleaf ta lashe zaben Liberia

Hakkin mallakar hoto REUTERSLucas JacksonFiles

Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben Liberia ta fitar ya nuna Shugaba mai ci, Ellen Johnson Sirleaf, na kan gaba tare da kashi casa'in cikin dari na kuri'un da aka kada.

Jama'a dai ba su fita da yawa ba, saboda kashi 33 ne cikin dari kawai suka fita, wani bangare saboda kiran kauracewa zaben da dan takarar yan adawa, Winston Tubman wanda ya yi zargin magudi a zagayen farko, yayi.

Mr. Tubman ya yi watsi da sakamakon zaben

Masu sa ido na kasashen duniya dai sun yi watsi da zargin sa.

Masu lura da al'amura sun ce kauracewar da kuma rashin fitowar jama'a zai shafar halaccin nasarar Mrs Sirleaf sannan kuma ya kara dada zaman zullumi.