Sudan ta Kudu ta zargi Sudan da kai hari

Hakkin mallakar hoto AFP

Sudan ta Kudu ta zargi makwabciyarta ta arewa, Jamhuriyar Sudan da yin ruwan bama bamai ta jiragen saman yaki a kan wani sansanin yan gudun hijira a kudancin kan iyaka.

Mazauna sansanin a garin Yida a cikin Jihar Unity, sun ce wani jirgin sama sanfarin Antonov ya yi shawagi a saman sansanin kafin ya jefa bama bamai biyar.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sunce mutane akalla 12 ne suka mutu.

Sansanin yana tsugunar da yan gudun hijira daga rikicin kudancin Kordofan, wanda ke a arewacin kan iyaka.

Gwamnan Jihar ta Unity, ya ce ya kamata a rike Shugaba Omar al -Bashir da alhakin kai harin bam din.

Tashin hankali a kan iyaka tun samun yancin kan Sudan ta Kudu ya tayar da zaman dar dar tsakanin kasashen biyu.