Mummunar girgizar kasa ta afkawa Turkiyya

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Ma'aikatan ceto a birnin Van na kasar Turkiyya

A kasar Turkiyya, ma'akatan agaji na ci gaba da aikin zakulo mutane daga baraguzan gine-gine a birnin Van, bayan wata mummunar girgizar kasa ta aukawa yankin.

Girgizar kasar, wacce ke da karfin maki biyar, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama cikinsu har da manema labarai, da masu aikin bayar da agaji, wadanda suka je yankin don gudanar da aiki.

Wani mamba a majalisar dokokin kasar, Nasmi Guhr, wanda ke birnin na Van a lokacin da lamarin ya faru, ya bayyana abin da ya faru:

''Ina gaban daya daga cikin gine-ginen da suka fadi. Wani otel ne, kuma abin takaici shi ne kusan mutane arba'in sun mutu''.

Koda a makonni biyun da suka gabata, wata girgizar kasa a yankin ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane dari biyar.