An tarwatsa masu zanga zanga a Abuja

Jami'an tsaro a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

Jami'an tsaro a Nijeriya sun tarwatsa wasu mutane da suka taru don yin zanga zanga akan shirin gwamnatin kasar na janye tallafin da take baiwa bangaren man fetur.

Mutanen dai sun yi yunkurin gudanar da kwatankwacin zanga zangar nuna adawa da shirin tattalin arzikin gwamnatoci ne da ake yi biranen London da New York.

Masu zanga zangar, su kimanin dari, sun taru ne a dandalin Unity Square dake Abuja, amma sai jami'an tsaro suka bukaci duk su watse.

Hukumomin sun ce sun tarwatsa taron ne domin kare lafiyar matasan, saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar.

Karin bayani