Za a yi gangami game da cire tallafin mai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, yau Juma'a ne ake sa ran wasu kungiyoyin matasa za su fara wani salon zaman dirshan na nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin kasar na janye tallafin albarkatun man fetur.

Kungiyoyin matasan dai suna amfani ne da kafar sadarwa ta Internet wajen samun magoya baya ga wannan shiri na su da suka yiwa lakabi "Occupy-Abuja".

Za a gudanar da gangamin ne a dandalin hada kan kasa da ke tsakiyar birnin Abuja.

Ita dai gwamnati ta ce za ta janye tallafin ne domin ba ya kaiwa ga talakawa, sai dai kungiyoyin sun ce ba haka batun ya ke ba.