Sabon Firayim Ministan Girka ya bayyana manufofinsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lucas Papademos

Sabon Firayim ministan kasar Girka, Lucas Papademos, ya ce wajibi ne kasar ta samu kashi na gaba na tallafin kudin da kasashen duniya suka yi alkawarin ba ta.

Mr Papademos ya ce hakan ne zai sa kasar ta fita daga kangin tattalin arzikin da take ciki.

Ya kara da cewa wannan shi ne babban abin da gwamnatinsa za ta sanya a gaba.

Ya ce bashin da ya yiwa kasar katutu ya jefa ta cikin mummunan hali, sannan ya yi kira ga 'yan kasar da su hada kawunansu.

Pia Hansen, ita ce kakakin Hukumar Tarayyar Turai, ta ce yana da matukar muhimmanci a samu gwamnatin hada kai a Girka, wacce za ta fitar da ita daga halin da ta fada a ciki.