Majalisar dokokin Italiya za ta yi muhawara kan tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi

A yau Juma'a ne majalisar dokokin kasar Italiya za ta fara muhawara kan matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar domin shawo kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Ana sa ran majalisar dattawa za ta amince da shirin, sannan ta wakilai ta biyo bayanta a karshen mako.

Alkawarin yin murabis din da Firayim Minista Silvio Berlusconi ya yi kuma zai biyo.

Rahotanni dai na cewa, wani masanin tattalin arziki kuma tsohon kwamishina a Tarayyar Turai, Mario Monti, ne zai maye gurbinsa.

Masana sun yaba

Masana na ganin wadannan matakai za su bunkasa tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal.

Da ma dai shugaban kasar Italiya, Giorgio Napolitano, ya tabbatar wa da kasuwannin kudi na duniya cewa, kasarsa za ta iya shawo kan matsalar bashin da ke addabarta.

Shi kuwa Firayim Minista, Silvio Berlusconi, ya ce zai yi murabus idan har majalisar dokokin kasar ta amince da sauye-sauye a kan kasafin kudin kasar.

Karin bayani