Kotu ta yankewa sojin Amurka hukunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Amurka

Wata kotu da ke birnin Washington na Amurka ta yankewa wani sojin kasar hukuncin daurin rai-da-rai bayan ta same shi da laifin kisan fararen hula a Afghanistan.

Sojan, maisuna Sajant Calvin Gibbs, ya kashe wasu mutane guda uku da basa dauke da makamai, a yayin da tawagar da yake jagoranta ke aikin sintiri a lardin Kandahar na Afghanistan a bara.

An tuhumi Sajant Gibbs da aikata laifuka uku, da suka hada da kitsa kisa, da yanke 'yan yatsun mutanen da ya kashe, da kuma ajiye kasusuwa da ma hakoran mutanen a matsayin wata ganimar yaki.

An tuhume shi ne tare da wasu sojoji guda uku.

Sojojin sun amince da aikata laifukan, sai dai sun roki kotun da ta yanke musu hukunci mai sassauci.