Yara na fama da tamowa a Agades, Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Taswirar Nijar

A jamhuriyar Nijar rahotanni daga jihar Agadas da ke arewacin kasar na cewa yara sama da dubu biyar ne suka kamu da tamowa, yayin da sama da arba'in daga cikinsu suka rasu, daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu.

Ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan agaji OCHA reshen jihar Agadas ne ya yada labarin, kuma hukumomin kiwon lafiya na kasar sun tabbatar da hakan.

Jihar ta Agadas dai na daga cikin yankunan da ke da gibi na abinci, sakamakon rashin kyawon damunar bana; bugu da kari jihar ta fuskanci matsalar kwararowar 'yan gudun hijira daga rikicin kasar Libya.

Karin bayani