Wasu abubuwa sun fashe a Tehran

Wani jami'in Iran ya ce, mutane goma sha biyar sun hallaka, yayin da aka samu wasu fashe fashe guda biyu, a wani sansanin soja da ke yammacin Tehran, babban birnin kasar.

Wani kakakin dakarun juyin juya halin Iran din, wadanda sune ke da sansanin, ya ce lamarin ya faru ne, yayin da sojoji ke kai albarusai daga wannan waje zuwa wancan.

Fashe fashen sun lalata yawancin sansanin, wanda dakarun juyin juya halin kasar ke amfani da shi.

An ce akalla daga nisan kilomita arba'in da biyar, an ji karar daya daga cikin fashe fashen.

Wani mutum da ke kusa da wurin ya ce, da wajen karfe goma zuwa goma da rabi na safe ne suka ji wata babbar kara da ta sa suka kidime.

Wani jami'in Iran din ya ce, hatsari ne, ba wai wata makarkashiya ce aka kulla ba.

Karin bayani