Majalisar wakilan Italiya na shirin tafka muhawara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dokokin Italiya

A yau Asabar ne majalisar wakilan kasar Italiya za ta tafka muhawara game da shirin tsuke-bakin aljihun gwamnatin kasar.

Bayanan da ke fito daga majalisar dai, sun nuna cewa da alama 'yan majalisar za su amince da shirin, bayan da takwarorinsu da ke majalisar dattawa suka amince da shi a jiya Juma'a.

Matakan sun hada da kara yawan shekarun da mutum zai yi kafin a fara bashi kudin fansho, da kara farashin man fetur, da gudanar da sauye-sauye a tsarin biyan haraji, da na mallakar gidaje.

Kuma da zarar sun amince da shirin, to ana sa ran Firayim Ministan kasar, Sylvio Berlusconi, zai sauka daga mukaminsa kamar yadda ya yi alkawari.

Kasar ta Italiya dai na fuskantar tabarbarewar tattalin arziki, irin wanda kasar Girka ke ciki, kuma hakan ne ya sanya hukumomi a kasar ke daukar matakan kaucewa wannan matsala.

An samu ci gaba

Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, Christine Lagarde, ta ce an samu ci gaba a kasashen Italiya da Girka domin samun daidaiton siyasa da manufofin tattalin arziki irin wadanda IMF da kasuwannin kudi ke bukata.

Karin bayani