Silvio Berlusconi ya sauka daga mukaminsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Berlusconi ya yi murabus daga mukaminsa na Fira Ministan Italiya

Shahararren mutumin da ya shafe kusan shekaru ashirin yana tasiri a harkokin siyasar kasar Italiya, Silvio Berlusconi, ya sauka daga mukaminsa na Firayim Ministan kasar.

Da ma dai Mr Berlusconi ya sha alwashin ajiye mukaminsa, muddun majalisun dokokin kasar suka amince da shirin gwamnati na tsuke bakin aljihunta, wadanda ake ganin sune za su magance matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Sakatare Janar na ofishin shugaban kasar Italiya, Donato Marra, ne ya sanar da saukar Mr Silvio Berlusoni.

Ya ce: '' A yau, Silvio Berlusconi ya bakonci shugaba Giorgio Napolitano, a fadar shugaban kasa, kuma ya mika masa takardar sauka daga mukaminsa, bayan da ya sanya hannu a kan wata doka da za ta daidaita harkokin kudin kasa.Kuma shugaban kasa ya gode masa''.

'Yan Italiya na murna

Bayan wannan sanarwar ce, tsohon Firayim Ministan, ya fice daga fadar shugaban kasar.

A wajen fadar kuwa, mutane ne suka yi dandazo suna jiran fitowar Mr Berlusconi, suna ta kade-kade da wake-wake don bayyana murnarsu da saukar tasa.

Sun yi ta yi masa ihu, suna jifan motar da ya ke ciki.

Wasu sun bayyana shi da cewa shi barawo ne, wasu ko cewa suka yi dan daba ne.

Mr Belusconi dai, wanda hamshakin dan kasuwa, kuma mamallakin kafafen yada labarai da dama, ya shafe kusan shekaru ashirin yana tasiri a harkokin siyasar Italiya.

Ya taba bayyana kan sa da cewa shi ne Firayim Minista mafi kwazo da kasar ta samu, tun bayan hadewarta shekaru dari da hamsin din da suka gabata.

Mr Belusconi ya sha musanta cewa kasar na cikin mummunan yanayin tattalin arziki.

Wani shahararren masanin tattalin arziki, Mario Monti ne dai zai maye gurbin Mr Berlusconi.

Karin bayani