Syria ta nemi ganawa da kasashen larabawa

Syria ta kira taron taron gaggawa na kasashen larabawa, domin duba hanyoyin magance rikicin da kasar ke fama da shi.

Kwana daya bayan da kungiyar kasashen larabawan ta dakatar da Syrian, saboda ta kasa aiwatar da wata yarjajeniyar kawo zaman lafiyar da aka cimmawa a farkon wannan watan, mahukuntan Syrian sun ce har yanzu suna goyon bayan shirin kawo zaman lafiyar.

Shugabannin na Syria sun yi kira ga kungiyar kasashen Larabawan da ta tura wata tawagar ministoci zuwa kasar, domin ta kula da yadda ake aiwatar da yarjajeniyar kawo zaman lafiyar.

Tun farko kasar Masar ta bukaci Syrian da ta mutunta yarjajeniyar, domin a samu a janye dakatarwar da aka yi mata.

A wani bangaren kuma, Turkiyya tayi kira ga hukumomin Syriar da su tabbatar da tsaron jami'an diplomasiyya a kasar, bayan da a jiya aka kaiwa ofishin jakadancinta hari a birnin Damascus, tare da na kasashen Saudiyya da Qatar.